Tsohon dan wasan Japan, Masato Kudo, ya rasu
Masato Kudo ya rasu ne ranar Juma’a, sakamakon rashin lafiya, bayan an yi masa tiyata a kwakwalwa.
Tsohon dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar kasar Japan, Masato Kudo, ya rasu yana da shekara 32.
Masato Kudo ya rasu ne ranar Juma’a, sakamakon rashin lafiya, bayan an yi masa tiyata a kwakwalwa.
Masato Kudo ya murza leda a gasa J-League na kasar Japan da gasar Major League Soccer da kuma ta kasar Australia.
Kafin rasuwarsa yana wasa ne a kungiyar Tegevajaro Miyazaki da ke rukuni na uku a kasar Japan.
Kudo ya lashe gasar J-League a lokacin yana kungiyar Kashiwa Reysol a 2011, kuma sau hudu yana yi wa kasarsa wasa, wadanda a ciki ya zura kwallaye biyu.
Ya kuma yi wasa a kungiyar Vancouver Whitecaps a gasar MLS da kuma Brisbane Roar a gasar A-League.
Kungiyar Tegevajaro ta bayyana shi a mtsayin “dan wasa da ya yi nasara” wanda kuma “ba shi da girman kai, kuma mutm ne da ya san darar abokan wasarsa da kungiya da kuma magoya bayan”.
Kocin Brisbane, Warren Moon ya ce: “Mutumin kirki ne wanda ba ya makara zuwa atisye, kuma kullum a cikin annashuwa yake.
“Ma a yi kewarsa matuka, muna jajanta wa matarsa da ’yarsu.“