Tsohon Daraktan yakin neman zaben Gwamnan Gombe ya koma NNPP
Shi ne Daraktan kamfen din Gwamnan a 2011 da 2015
Tsohon Daraktan yakin neman zaben Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe a zabukan shekara ta 2011 da 2015, Musa Zubairu, ya fice daga jam’iyyar APC ya koma NNPP.
Tsohon Daraktan ya ce ya koma jam’iyyar NNPP ne tare da dimbin magoya bayansa inda ya ce ya koma jam’iyyar ne don ya taya dan takarar Gwamna na jam’iyyar, Khamisu Ahmed Mailantarki, yakin neman zabensa dan ya samu nasarar lashe shi.
- Kotu ta dakatar da Ganduje daga sayar da wani asibiti a Kano
- Za a kafa dokar daurin shekara 5 ga masu yi wa mata kaciya
Dan takarar gwamnan na NNPP Khamisu Ahmed Mailantarki ne ya karbi tsohon Daraktan tare da Shugaban jam’iyyar na jihar Gombe, Abdullahi Maikani a Gombe ranar Alhamis.
Har ila yau, wakilinmu ya rawaito cewa yanzu haka akwai ’yan majalisar Dokokin Jihar guda uku da suka bar jam’iyyarsu ta APC suka koma NNPP.
Da yake jawabi bayan karbar wadanda suka canja shekar, Khamisu Mailantarki, ya jinjina musu inda ya ce a kwanakin nan ne ma jam’iyyar ta karbi dubban ’ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da na PDP da suka canja sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Daga nan sai dan takarar ya ce yana da yakinin a shekarar 2023 jam’iyyar su za ta iya lashe zaben da za a gudanar.