Tsohon duniya mai shekara 145 na neman mutuwa

Wani mutumin kasar Indonesiya da ya fi kowa tsufa a duniya, bisa la’akari da yawan shekarunsa da suka kai 145, ya bayyana cewa, a shirye yake ya mutu.A kundin bayanai da jami’an kasar Indonesiya suka tattara, an yi nuni da cewa Mba Gotho yana da shekara 145, kuma an haife shi a ranar 31 ga […]

Tsohon duniya mai shekara 145 na neman mutuwa
Tsohon duniya mai shekara 145 na neman mutuwa

Wani mutumin kasar Indonesiya da ya fi kowa tsufa a duniya, bisa la’akari da yawan shekarunsa da suka kai 145, ya bayyana cewa, a shirye yake ya mutu.
A kundin bayanai da jami’an kasar Indonesiya suka tattara, an yi nuni da cewa Mba Gotho yana da shekara 145, kuma an haife shi a ranar 31 ga Disambar 1870. Ya ce bai yi mamakin ganin daukacin ’yan uwansa na haihuwa su 10 duk sun mutu, har ma da matansa hudu, in data karshensu ta mutu cikin shekarar 1988
daukacin ’ya’yansa duk sun mutu,. Kuma yana zaune ne tare da jikokinsa da tattaba kunnensa da ’ya’yan tattaba kunnen.
Matukar aka tantance hakikanin gaskiyar wannan lamari, to tabbas ya fi kowa tsufa a duniya, tunda yanzu kambin nisan shekaru da tsufa na hannun wata ‘’yar kasar Faransa, mai Suna Jeanne Calment mai shekara 122. Wannan tsoho tukuf-tukuf ya fito daga ga Sragten da ke tsakiyar yankin Jaba, kuma gidan talabijin na Lipitan 6 ya tattauna das hi.
Ya ce ya dade yana raye a haka, shi yasa ba zai damu ba, idan mutuwa ta riske shi. Bukatata kawai in mutu, tunda daukacin jikokina suna iya kula da kansu ne, kamar yadda ya bayyana wa tashar talabijin ta Liputan 6 a Talatar makon jiya. Suryanto, jikan Mbah Gotho ya ce kakansa ya dade da shirya wa mutuwa, tun yana da shekara 122, amma har yanzu al’amarin bai auku ba. Acewarsa: “an haka masa kabari tun a shekarar 1992, yau shekara 24 ke nan.” Baya ga haka, Suryanto ya ce iyalan Mbah tuni suka ware masa wurin da za a yi masa kabari kusa da kaburburan ’ya’yansa. Wani jami’in sashen tattara bayanai a kasar Indonesiya ya tabbatar da ranar haihuwar Mbah Gotho, kamar yadda take a rubuce jikin katinsa, wato 31` ga Disambar 1870.
Ko an ki ko an so dole a sanya shi a jerin mutanen da suka fi tsufa da nisan shekaru a wannan duniyar, duk da cewa masu bincike na daban ba su tantance hakikanin lamarin ba.
A cewar jikokinsa, ’yan kwanakin nan ya fi sauraren rediyo, domin idanunsa ba su da kwarin kallon talabijin. Kimanin shekaru uku ken an da suka gabata aka fara dura masa abinci, tare da yi masa wanka, saboda rashin kwarin jikinsa.
Da aka tuntubi Mbah Gotho kan ko mene ne sirrin tsawon rayuwarsa, sai ya bayar da amsar cewa: Sirrin dai hakuri ne kawai.’