Tsohon Editan Aminiya ya zama kakakin Gwamnan Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya nada tsohon Editan jaridar Aminiya kuma Manajan Bunkasa Kasuwanci na kasa na Kamfanin Media Trust Malam Bello Muhammad Zaki a matsayin Mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai. Wata sanarwa dauke da sanya hannun Sakataren Gwamnatin Jigawa Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ta ce nadin ya fara […]
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya nada tsohon Editan jaridar Aminiya kuma Manajan Bunkasa Kasuwanci na kasa na Kamfanin Media Trust Malam Bello Muhammad Zaki a matsayin Mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Sakataren Gwamnatin Jigawa Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
An haifi Bello Zaki a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa a ranar 10 ga Disamban 1960, inda ya halarci makarantu daban-daban da suka hada da Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Warri da ke Jihar Delta daga 1975 zuwa 1980 da Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Kano inda ya samu babbar Diploma a fannin Akanta a 1985. Sannan yana da babbar takardar shaida kan aikin jarida da kula da kudi da kuma harkokin mulkin jama’a.
Wakili ne a Cibiyar kwararru kan Tattalin Arziki ta Najeriya da Cibiyar Kudi da Nazarin Zuba Jari da kuma Cibiyar kwararru kan Gudanar da Mukamai da sauransu.
Bello Zaki ya fara aiki a matsayin akanta da Ma’aikatar Kudi ta Jihar Kano, sai kuma Kamfanin kwararru kan aikin Akanta na Muhtari Dangana and Co. Chartered Accountants.
Ya yi Editan jaridar Aminiya na tsawon shelara shida, kafin a nada shi Manajan Harkokin Kasuwanci na Daily Trust sama da shekara daya da ta gabata.