Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi ya riga mu gidan gaskiya

A cikin watan Afrilu, Berlusconi ya yi fama da ciwon huhu.

Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi ya riga mu gidan gaskiya

Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi, ya mutu yana da shekaru 86, bayan fama da rashin lafiya.

Hamshakin attajirin da ya mallaki kafar watsa labarai ya mutu ne a asibitin San Rafaelle da ke birnin Milan.

Attajirin kuma dan gaye, ya soma jagorantar Italiya ne a shekarar 1994, sannan kuma ya ci gaba da jan zarensa a lokuta daban-daban har zuwa shekara ta 2011.

Berlusconi ya jagoranci jam’iyyar Forzia Italia wajen shiga gwamnatin hadin gwiwa inda daga bisani aka zabe shi a matsayin dan Majalisar Dattawa a watan Satumbar bara.

Kafin mutuwarsa, Berlusconi ya jagoranci gwamnatocin Italiya daban daban tsawon fiye da shekaru 9.

Lokutan da marigayin ya jagoranci gwamnatocin kasar ta Italiya sun hada da shekarar 1994 zuwa 1995, sai kuma 2001 zuwa 2006, da kuma shekarar 2008 zuwa 2011.

Tun shekarar 2019 har zuwa lokacin mutuwarsa, Silivio Berlusconi ya ke zauren Majalisar Dokokin Italiya, mukamin da ya taba rikewa a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.

A watannin baya, tsohon Firaministan na Italiya ya sha fama da cutuka da dama, cikinsu kuma har da annobar Coronavirus a shekarar 2020.