Tsohon Firayi Ministan Habasha ya bukaci masu zuba jari na Afirka su yi koyi da Dangote

Tsohon Firayi Ministan Kasar Habasha Mista Hailemariam Desalegn, ya bayyana cewa Matatar Dangote ta zama zakaran gwajin dafi, saboda irin gagarumin jari da yake zubawa a hakar tace man fetur, ya kuma kalubalanci sauran masu zuba jari su yi koyi da Dangote wajen zuba jarinsu a Nahiyar Afirka. Da yake jawabi  lokacin da ake zagayawa […]

Tsohon Firayi Ministan Habasha ya bukaci masu zuba jari na Afirka su yi koyi da Dangote

Daga hagu Aliko Dangote da Hailemariam da Debakumar

Tsohon Firayi Ministan Kasar Habasha Mista Hailemariam Desalegn, ya bayyana cewa Matatar Dangote ta zama zakaran gwajin dafi, saboda irin gagarumin jari da yake zubawa a hakar tace man fetur, ya kuma kalubalanci sauran masu zuba jari su yi koyi da Dangote wajen zuba jarinsu a Nahiyar Afirka.

Da yake jawabi  lokacin da ake zagayawa da shi cikin harabar matatar mai dauke da bangaren takin zamani, Mista Desalegn ya ce Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote yana da matukar sha’awar zuba jari a harkar mai wannan ya sa harbakar tatalin arziki take samun tagomashi a Afirka.

Ya ce Nahiyar Afirka tana  bukatar masu zuba jari kamar yadda Dangote yake yi a halin yanzu. “Ina ganin wannan babban darasi ne ga masu dukiya na Afirka cewa su dauki kasada irin ta Dangote wajen zuba jari a nahiyar, domin yin hakan yana bukatar sadaukarwa da jajircewa,” inji shi.

Ya ce, “Ina tabbatar da cewa wannan matata ba Najeriya ce kadai za ta amfana ba duk kasashen Afirka za su amfana da wannan matata.”

Da yake karin haske a kan aikin matatar Shugaban Sashin Tsare-Tsare da Ci gaban Manyan Ayyuka na Kamfanin Dangote Mista Debakumar Edwin ya ce aikin matatar zai bunkasa harkoki kusan dubu 135, da gidajen mai dubu 26 da 716 da daffo-daffo guda 129 a fadin Najeriya sai kuma motocin dakon mai  2,600. Ya ce wannan matata za ta kuma samar da dimbin ayyukan yi ga ’yan Najeriya.