Tsohon Gwamnan Kaduna ya rasu

Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita ya rasu yana da shekara 85 a rayuwa. Tsohon gwamnan ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a wani asibiti da ke Abuja. Sakataren masarautar Katsina, Bello Ifo ne ya tabbatar da rasuwar, inda ya sanar da cewa za a yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin […]

Tsohon Gwamnan Kaduna ya rasu

Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita ya rasu yana da shekara 85 a rayuwa.

Tsohon gwamnan ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a wani asibiti da ke Abuja.

Sakataren masarautar Katsina, Bello Ifo ne ya tabbatar da rasuwar, inda ya sanar da cewa za a yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a fadar mai martaba sarkin Katsina.

Lawal Kaita ya yi gwamna ne a inuwar jam’iyar NPN a tsohuwar Jihar Kaduna a 1983 kafin sojoji su yi wa Shagari juyin mulki.

An haifeshi ne a ranar hudu ga watan Oktoba, shekarar 1932 a gidan sarautar Katsina. Ya yi Kwalejin Barewa da ke Zariya daga shekarar 1946 zuwa 1950, sannan ya je makarantar karatun tattalin arziki na Landan daga 1971 zuwa 1972.

Bayan ya dawo Najeriya, sai Kaita ya fara aiki a tsohuwar Jihar Kaduna har ya kai matsayin babban sakatare a ma’aikatan ayyuka a shekarar 1977.

Lawal Kaita ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya takwas da jikoki da dama.