Tsohon Gwamnan Kano na mulkin soja Dominic Oneya ya rasu
Tsohon Gwamnan Kano na mulkin soja a zamanin tsohon Shuaban Kasa Sani Abacha, Birgediya Dominic Obukadata Oneya mai ritaya ya rasu. Birgediya Oneya mai shekara 73 shi ne kuma tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF). An yi garkuwa da iyayen Shugaban Majalisar Zamfara Ali Kachalla: Dan bindigar da ya kakkabo jirgin yaki a […]
Tsohon Gwamnan Kano na mulkin soja a zamanin tsohon Shuaban Kasa Sani Abacha, Birgediya Dominic Obukadata Oneya mai ritaya ya rasu.
Birgediya Oneya mai shekara 73 shi ne kuma tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF).
- An yi garkuwa da iyayen Shugaban Majalisar Zamfara
- Ali Kachalla: Dan bindigar da ya kakkabo jirgin yaki a Zamfara
Daya daga cikin iyalan mamacin ne ya tabbatar mutuwar tashi ranar Alhamis da safe a gidanshi da ke Effurun, Karamar Hukumar Uvwie ta Jihar Delta.
Marigayin dan asalin Agborho ne da ke Karamar Hukumar Ughelli ta Arewa da ke Jihar Delta.
A zamanin tsohon Shugaban Kasa, Janar Sani Abacha ne Oneya ya zama Gwaman Kano na mulkin soja daga watan Agusta 1996 zuwa 1998.
Ya kuma yi Gwamnan Jihar Binuwai daga watan Agusta 1998 zuwa watan Mayu 1999 lokacin da gwamnatin soji ta Janar Abdulsalami Abbakar ta ba mika mulki ga fula a Najeriya.