Tsohon Gwamnan Oyo ya kafa gidan rediyon PARROT
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otumba Christopher Adebayo Alao Akala, ya bude wata tashar rediyo mai suna PARROT FM da za ta rika watsa shirye-shirye daga garin Ogbomoso, birni na biyu mafi girma a sasahen kudu maso Yammacin kasa. Bude wannan tashar rediyo da tsohon gwamnan ya yi a mahaifarsa Ogbomoso, yana da nasaba da yunkurin […]
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otumba Christopher Adebayo Alao Akala, ya bude wata tashar rediyo mai suna PARROT FM da za ta rika watsa shirye-shirye daga garin Ogbomoso, birni na biyu mafi girma a sasahen kudu maso Yammacin kasa. Bude wannan tashar rediyo da tsohon gwamnan ya yi a mahaifarsa Ogbomoso, yana da nasaba da yunkurin sake dawowa bisa karaga a zaben badi da ya fito gadan-gadan, inda ya fara neman amincewar al’ummar Jihar Oyo su mara masa baya.
Tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala na jam’iyar PDP, ya sha kaye ne a zaben shekara ta 2011 da APC tayi nasara. Ya shaida wa miliyoyin jama’a cewa, ya yanke shawarar sake dawowa bisa karagar mulki a matsayin Gwamna a zaben shekara ta 2015 ne, saboda lura da ya yi cewa, Gwamna Abiola Ajimobi na APC ya kasa shawo kan matsalolin da jama’a suke fuskanta a maimakon haka sai rushe-rushen shaguna da gidaje, ba tare da an biya diyya da samar da wani wuri daban ga irin wadannan mutane ba.
Da yake fadin haka a ranar Asabar da ta wuce a wajen wani gangami da magoya bayansa suka taru domin bude babban ofishin musayar ra’ayi da aka yi a Ibadan, tsohon Gwamnan, wanda uwargidansa Madam Oluwakemi Alao Akala ta wakilta, ya ce, yanzu haka akwai mutane maza da mata masu yawa da gwamnati mai mulki a jihar ta jefa su cikin mawuyacin hali ta fannin dakatar da harkokin kasuwancinsu, bayan an rusa musu wuraren da suke neman abinci, ba tare da an biya su diyya ko samar musu wani wuri daban ba.
A cewarsa: “Akwai da yawa daga cikin irin wadannan mutane sun tagayyara wasu ma sun rasa rayukansu a dalilin tsananin halin kunci da aka jefa su a cikin shekaru uku da mulkin kama karya a Jihar oyo.”
Ya ce, tausayin halin da irin wadannan mutane suke ciki shi ne babban dalilin da yasa ya yanke shawarar sake dawowa bisa karagar mulki, domin tsamo su daga halin ni ‘ya su.
Barrister Abraham Ojo, yana daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan, ya ce, “fitowar wasu ‘yan siyasa da suka yi fice a cikin jam’iyar PDP da suka dage a kan cewa dan asalin yankin Ibadan za a zaba a matsayin dan takarar gwamna a tutar PDP a zaben shekara ta 2015, ba zai hana tsohon Gwamna Alao Akala ci gaba da fafutikarsa ba, domin mun sani cewa, jama’a na goyon bayanmu. Kuma da yawa daga cikin wannan gungu na mutane bakwai ‘yan Ibadan da kowannensu yake so ya tsaya takarar kujerar gwamna a karkashin tutar PDP, sun yi haka ne, domin neman matsayi a nan gaba, amma ba domin yako wa jama’a ‘yanci ba.”