Tsohon gwamnan soji na Filato, Sanata Mana ya rasu
Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham ne, ya tabbatar da rasuwar.
Tsohon Gwamnan mulkin Soji na Jihar Filato, kuma Sanatan da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana, ya rasu.
Ya rasu ne da yammacin ranar Juma’a a Abuja, kwanaki biyu bayan sallamarsa daga asibiti.
- Tanka mai ta yi bindiga da mai yi mata gyaran walda
- Mutum 3 sun shiga hannu kan sace tagogin makaranta a Gombe
Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham ne, ya tabbatar da rasuwar a daren ranar Juma’a.
Mana, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Maiha a Jihar Adamawa, ya shugabanci Jihar Filato a matsayin shugaban mulkin soja daga Disamban 1993 zuwa Agustan 1996, a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
Daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Shugaban Ƙasa a lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar, kafin daga bisani ya zama Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa a shekarar 2007.
Kwaccham, ya ce marigayin ya rasu ya bar matansa da ’ya’yansa.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar a Masallacin Juma’a na Ƙasa da ke Abuja.