Tsohon kocin PSG Galtier ya samu aiki a Qatar

Tawagar ta ƙunshi tsohon ɗan wasan Liverpool da Aston Villa, Philippe Coutinho.

Tsohon kocin PSG Galtier ya samu aiki a Qatar

Tsohon kociyan Paris St-Germain Christophe Galtier ya maye gurbin Hernan Crespo a matsayin kocin ƙungiyar Al-Duhail ta Qatar.

Galtier, mai shekara 57, ya lashe gasar Ligue 1 da PSG a kakar wasa da ta wuce amma ƙungiyar ta yanke shawarar sallamarsa inda ta maye gurbinsa da tsohon kocin Barcelona Luis Enrique a watan Yuli.

A watan Disamba ne za a gurfanar da Bafaranshen gaban kotu, bayan wani bincike da aka yi kan zargin wariyar launin fata a lokacin da ya ke riƙe da mukamin kocin ƙungiyar Nice.

‘Yan sanda sun yi masa tambayoyi a watan Yuni kuma ya musanta zargin.

Galtier ya maye gurbin tsohon dan wasan Chelsea da Argentina Crespo, bayan ɗan wasan mai shekaru 48 ya raba gari da Al-Duhail ranar Laraba.

Ɗan Ƙasar Faransa Galtier ya taɓa zama gwarzon kocin Ligue 1 har sau uku kuma ya lashe babban gasar ta Faransa da Lille da kuma PSG.

Muƙamin da ya karɓa a Al-Duhail shi ne aikinsa na farko da zai yi a wajen Faransa kuma ya gaji tawagar da ta ƙunshi tsohon ɗan wasan Liverpool da Aston Villa, Philippe Coutinho.