Tsohon kocin Rangers ya koma Gabros

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles da kuma Enugu Ranger Mista John Obuh ya koma kulob din Gabros International da ke wasa a gasar rukuni-rukuni ta kasa da aka fi sani da Glo Premier League. Haka kuma zai yi aiki ne da mataimakinsa shi ma tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa […]

Tsohon kocin Rangers ya koma Gabros
Tsohon kocin Rangers ya koma Gabros

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles da kuma Enugu Ranger Mista John Obuh ya koma kulob din Gabros International da ke wasa a gasar rukuni-rukuni ta kasa da aka fi sani da Glo Premier League.

Haka kuma zai yi aiki ne da mataimakinsa shi ma tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 Fanny Amun a kulob din. Sannan Waidi Akanni, tsohon dan kwallon Super Eagles shi ma yana daga cikin mataimakan kocin.
Yayin da aka dauki Fanny Amun a matsayin babban jami’in da zai rika lura da yadda harkokin kulob din ke tafiya, shi kuwa Waidi Akannni an dauke shi ne a matsayin jami’in tuntuba (consultant).
Shi kuma Bature dan asalin Beljiyam an tabbatar masa da mukamin Babban Mai Ba Da Shawara (Technical Adbiser) ga kulob din ne. An gudanar da wadannan canje-canje a kulob din ne bayan Ifeanyi Ubah ya saye kulob din.
Kulob din Gabros dai yana hankoron ya zama daya daga cikin kulob hudu da za su kasance a saman tebur din gasar rukunin firimiya ta Najeriya a wannan shekara. Kawo yanzu kulob din ne na biyu a teburin na firimiya da maki 13 biye da kulob din Giwa FC da ke na daya.