Tsohon Kocin Super Eagles ya rasu
Hukumar Kwallon Kafar Kasar nan (NFF) ta ce tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, wanda kuma ya taba zama kocin kungiyar, Stephen Okechukwu Keshi, ya rasu. Mista Keshi ya rasu ne da tsakar daren ranar Talata a birnin Benin da Jihar Edo, kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Twitter. […]

Hukumar Kwallon Kafar Kasar nan (NFF) ta ce tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, wanda kuma ya taba zama kocin kungiyar, Stephen Okechukwu Keshi, ya rasu.
Mista Keshi ya rasu ne da tsakar daren ranar Talata a birnin Benin da Jihar Edo, kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Twitter. Sai dai ba ta bayyana abin da ya yi ajalinsa ba, sai dai rahotanni na cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.
An haifi marigayin ne a ranar 23 ga watan Janairun shekarar 1962 a garin Azare na Jihar Bauchi.