Tsohon Kwamandan Al-Shabab ya la’anci ayyukan ta’addanci na kungiyar

Wani tsohon kwamandan kungiyar Al-Shabbab da ke kasar Somaliya Zakariyya Isma’il Hersi ya fito fili ya ce ya daina ayyukan ta’adanci kuma ya yi Allah wadai da rikicin da abokansa na kungiyar ke haddasawa. Zakariyya Isma’il Hersi wanda ya taba zama babban jami’in leken asiri na kungiyar Al-Shabbab wadda ke da alaka da kungiyar Alka’ida […]

Tsohon Kwamandan Al-Shabab ya la’anci ayyukan ta’addanci na kungiyar
Tsohon Kwamandan Al-Shabab ya la’anci ayyukan ta’addanci na kungiyar

Wani tsohon kwamandan kungiyar Al-Shabbab da ke kasar Somaliya Zakariyya Isma’il Hersi ya fito fili ya ce ya daina ayyukan ta’adanci kuma ya yi Allah wadai da rikicin da abokansa na kungiyar ke haddasawa.

Zakariyya Isma’il Hersi wanda ya taba zama babban jami’in leken asiri na kungiyar Al-Shabbab wadda ke da alaka da kungiyar Alka’ida ya mika kansa ne ga jami’an gwamnatin Somaliya a watan Disamban bara.
Ya ce “Daga yau zan rika bayyana ra’ayoyina da akidojina ta hanyar lumana da fahimta.” Hersi ya yi wannan furucin ne a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Mogadishu a ranar Talata.
Da ya juya kan abokansa na kungiyar Al-Shabbab Hersi ya ce “Ina gargadinku abokaina ku nemi warware matsalolinku ta hanyar lumana da tattaunawa cikin kwanciyar hankali.”
Idan ba a manta ba a watan Yunin shekarar 2012, Amurka ta ba da tayin tukuicin Dala miliyan uku, (kimanin Naira miliyan 600) ga duk wanda ya bayar da labarin da zai kaiga kama Zakariyya Hersi.
Ana zargin Hersi da kasancewa na hannun daman Ahmed Abdi Godane tsohon shugaban kungiyar Al-Shabbab.