Tsohon Kwamishinan Gombe, Ibrahim El-Hassan Kwami ya rasu

Gwamnan jihar ya bayyana alhininsa game da rasuwar tsohon Kwamishinan.

Tsohon Kwamishinan Gombe, Ibrahim El-Hassan Kwami ya rasu

Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim El-Hassan Kwami, kuma Sarkin Sudan na Kwami, ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa kan rasuwar marigayin, tare da jajanta wa iyalansa, al’ummar Kwami da ɗaukacin al’ummar jihar.

A wata sanarwa da Darakta Janar na Harkokin Yaɗa Labaran Gidan Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya ce marigayin ya kasance jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya ba da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Ya ce a lokacin da Ibrahim El-Hassan Kwami yake Kwamishinan Yaɗa Labarai, ya gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa, gaskiya da sadaukarwa.

Gwamnan, ya kuma yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar a Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa, inda ya yi aiki har ya kai matsayin babban jami’i.

Ya ce rasuwar Alhaji Ibrahim El-Hassan Kwami babban rashi ne ga iyalansa, al’ummar Kwami, Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Gwamna, ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa haƙurin rashinsa.