Tsohon Kwamishinan labarai na Gombe ya rasu
Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda.
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu.
Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara.
- Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata
- Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya
Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar marigayin.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya ce Julius Ishaya, mutum ne nagari mai basira da jajircewa.
Hakazalika, ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar, musamman kafin kafa gwamnatinsa.
Ya ce a lokacin da Ishaya yake Kwamishinan Matasa, daga baya kuma na labarai da al’adu, ya nuna ƙwarewa da hangen nesa tare da bayar da gudunmawar da ta amfani majalisar zartarwar jihar.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Gombe, iyalan marigayin, abokansa, da kuma ɗaukacin al’ummar Masarautar Kaltungo.
Ya roki Allah ya jikan mamacin, ya kuma ba iyalan sa hakurin jure wannan babban rashi.