Tsohon kwamsihina mai neman uwa da ’ya ya shiga hannun kan fyade

A karshen makon jiya ne ’yan sanda a Jihar Kuros Riba suka kama tsohon Kwamishinan Watsa Labarai, Edet Okon Asim bisa zarginsa da yi wa wata yarinya daliba a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kalaba fyade. Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa mahaifiyar yarinyar Misis Stella farkar Mista Edet Asim ne yayin da yake […]

Tsohon kwamsihina mai neman uwa da ’ya ya shiga hannun kan fyade
Tsohon kwamsihina mai neman uwa da ’ya ya shiga hannun kan fyade

A karshen makon jiya ne ’yan sanda a Jihar Kuros Riba suka kama tsohon Kwamishinan Watsa Labarai, Edet Okon Asim bisa zarginsa da yi wa wata yarinya daliba a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kalaba fyade.

Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa mahaifiyar yarinyar Misis Stella farkar Mista Edet Asim ne yayin da yake nuna kansa a matsayin sauryin yarinyar.

Wata majiya ta kusa da iyalan Stella da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce yadda asirin wanda ake zargi ya tonu shi ne “ya shafe tsawon lokaci yana soyayya da mahaifiyar yarinyar, kuma yana neman yarinyar alhali mahaifiyar yarinyar tana sane. Sau uku ke nan ana zubar wa yarinyar ciki kuma da sanin uwar, wannan karo Edet Okon ya umarci uwar yarinyar da zubar da cikin, to amma a kokarin zubarwar ce har mahaifar yarinyar ta tabu,” inji majiyar

Okon Asim tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kalaba ne kuma Mataimaki na Musamman kan Harkokin Muhalli ga Gwamna Ben Ayade.

Wata majiya da ke kusa da wanda ake zargin da take kokarin karbar belinsa ta ce “Tuggu ce ta siyasa aka shirya masa, don haka karya ake yi masa.”

DSP Irene Ugbo Kakakin ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta ce “Gaskiya ce an kama shi bisa zargin yi wa wata yarinyar fyade, kuma yana hannunmu ana bincikensa.”