Tsohon ma’aikacin FRSC a Ibadan ya rasu

Ranar Juma’a ce Allah Ya yi wa Alhaji Abubakar Bawa, tsohon ma’aikacin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) rasuwa a Ibadan. Marigayin mai shekaru 66, ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya 7 tare da babban yayansa, Tukuran […]

Tsohon ma’aikacin FRSC a Ibadan ya rasu

Ranar Juma’a ce Allah Ya yi wa Alhaji Abubakar Bawa, tsohon ma’aikacin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) rasuwa a Ibadan. Marigayin mai shekaru 66, ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya 7 tare da babban yayansa, Tukuran Ibadan, Alhaji Aminu Yahya.
Limamin masallacin Juma’a na Unguwar Sabo Ibadan, Sheikh Rufa’i Hussaini shi ne ya jagoranci daruruwan musulmi da suka sallaci gawar marigayin jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a harabar babban masallacin. Wasu manyan jami’an Hukumar FRSC da ke Ibadan suna daga cikin daruruwan mutane da suka fara kai gaisuwar ta’aziyarsu zuwa gidan Alhaji Aminu Yahya, daya daga cikin dattijan Hausawan Ibadan, wanda ya jagoranci iyalan marigayin da sauran ’yan uwa domin zaman makoki.