Tsohon madugun ’yan tawaye ya kafa kungiyar neman mai da Bazoum kan mulkin Nijar

Rhissa Ag Boula, ya kafa wata kungiyar fafutukar maido da Bazoum Mohammed kan kujerar shugabancin kasar a siyasance.

Tsohon madugun ’yan tawaye ya kafa kungiyar neman mai da Bazoum kan mulkin Nijar

Wani tsohon shugaban ’yan tawaye a Nijar, wanda a yanzu ya zama jagora a siyasa, Rhissa Ag Boula, ya kafa wata kungiyar fafutukar maido da Bazoum Mohammed kan kujerar shugabancin kasar a siyasance.

Rhissa Ag Boulay a bayyana kafa kungiyar ta ‘Council of Resistance for the Republic’ CRR ce cikin wata sanarwa da ta bayyana a yau Laraba.

Sanarwar ta ce kungiyar ta CRR za ta bayar da gudunmawa ga dukkanin yunkurin da kasashe ke yin a ganin an mayar da Jamhuriyar Nijar zuwa karkashin mulkin dimokaradiya.

Wannan dai shi ne karo na farko da wani ya fito karara tare da yunkurin kalubalantar juyin mulkin da sojoji suka yi wa Bazoum Mohammed a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa