Tsohon magajin garin Maradi ya kafa sabuwar jam’iyya

Fiye da wata uku ke nan da tsige Malam kasim Muktar magajin garin Maradi da ke jamhuriyar Nijar. Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa an tsige magajin garin ne bisa ga zargin laifuka biyu wato: “kan batun kwamitin da zai raba shagunan sabuwar kasuwar zamani da aka kammala a garin, sai kuma […]

Tsohon magajin garin Maradi ya kafa sabuwar jam’iyya
Tsohon magajin garin Maradi ya kafa sabuwar jam’iyya

Fiye da wata uku ke nan da tsige Malam kasim Muktar magajin garin Maradi da ke jamhuriyar Nijar.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa an tsige magajin garin ne bisa ga zargin laifuka biyu wato: “kan batun kwamitin da zai raba shagunan sabuwar kasuwar zamani da aka kammala a garin, sai kuma maganar shuwagabanin uwar jam’iyar shi ta RSD (Gaskiya) da ke korafin ba ya girmamasu kuma ba ya cika alkawari.”
Ana cikin wannan yanayin ne sai kwatsam tsohon magajin garin ya fitar da ta shi sabuwar jam’iyyar, mai suna CPR (Inganci). Da wakilinmu yake zantawa da wani tsohon gogaggen dan siyasa Alhaji Rabe dan Legas kuma jigo a jam’iyyar RSD (Gaskiya) da yaje wurin tarbon magoya bayan wannan sabuwar jam’iyyar. Ya ce sun sauya sheka zuwa wannan sabuwar jam’iyyar ne ganin yadda aka hada kai da shugaban jam’iyyar RSD Malam Sehu Amadu aka ci amanar mutanan jihar Maradi. Ya ci gaba da cewa “mun fito ne kwanmu da kwarkwatanmu ne domin mu nuna wa duniya cewa wannan bawan Allah shi muke kauna domin shi ya zama zakaran gwajin dafi ga dukkannin gwamnonin da aka taba yi a tarihin jihar Maradi. Ganin farin jinin da yake da shi wurin al’uma da ayyukan ci gaba da samun karbuwa fiye da kowa, ya sa da mayan ’yan kasuwa da ‘yan siyasa suka dinga kai-kawo dan ganin an rabashi da wannan kujerar.