Tsohon Mataimakin Editan Daily Trust na cikin wadanda harin bam din Abuja ya halaka
Tsohon Mataimakin Editan Jaridar Daily Trust, Malam Sulaiman Maina Bisallah na daga cikin mutum 21 da suka halaka a harin bam din da aka kai shagunan Emab Plaza da ke kusa da shagunan Baned Plaza a Wuse 2, Abuja a shekaranjiya Laraba.Yayansa Muhammadu Maina Bisalla da ke aiki a Majalisar Dokoki ta kasa ne ya […]

Tsohon Mataimakin Editan Jaridar Daily Trust, Malam Sulaiman Maina Bisallah na daga cikin mutum 21 da suka halaka a harin bam din da aka kai shagunan Emab Plaza da ke kusa da shagunan Baned Plaza a Wuse 2, Abuja a shekaranjiya Laraba.
Yayansa Muhammadu Maina Bisalla da ke aiki a Majalisar Dokoki ta kasa ne ya tabbatar wa Aminiya haka ta tarho.
Ya ce sun fara shirye-shiryen karbo gawar marigayin don yi masa jana’iza a jiya Alhamis.Marigayi Suleiman Bisallah ya yi aiki a kamfanin Daily Trust a tsakanin shekarar 2007 zuwa farkon wannan shekarar lokacin da ya bar kamfanin ya koma wata sabuwar jarida mai suna ‘‘The Telegraph.’’
Harin dai ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma, kamar yadda wani ma’aikacin Masallacin Usman Bin Affan da ke daura da inda lamarin ya faru wanda na cikin wadanda suka yi jigilar wadanda lamarin ya shafa mai suna Muhammad Sharfilu Shitu, ya shaida wa Aminiya.
’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 21, kuma Kakakin Hedkwatar ’Yan sanda na kasa Franl Mba ya ce motoci 17 sun kone a harin bam din.
Wakilinmu ya ce maharan sun kai harin ne a kan irin manyan baburan nan da ake wasa da su.
Maza da mata, Musulmi da Kirista sun ruga cikin masallacin don neman mafaka, inji wani ganau da ya ce sun yi sawu biyu na majinyata da motocin hukumar masallacin.
Lokacin da wakilinmu ya je Asibitin Maitama da ya fi kusa da wurin da lamarin ya auku, ya ga jami’an jinya na kula da wadanda harin ya shafa, yayin da ake kula da wasu a barandar asibitin.
Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) sun ci gaba da jigilar majinyata a motocinsu da motocin Hukumar FRSC da na asibitin, har zuwa karfe 6:00 na yamma. Wani jami’in jinya ya tabbatar wa ’yan jarida cewa an kai gawar mutum tara asibitin da kuma wasu sassan jikin mutane, yayin da aka kai mutum 36 da suka samu raunuka.
Sojoji da ’yan sanda da na farin kaya sun rufe kofar shiga asibitin sakamakon tururuwar jama’a da ke neman shiga wurin in ban da ’yan jarida don magance cinkoso da samar da tsaro.
Wani jami’in Hukumar NEMA da bai bayyana sunansa ba ya ce, baya ga Asibitin Maitama, an kai wasu asibitocin Wuse da Garki da Asokoro da Asibitin kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya shaida wa jaridar Premium Times cewa sojoji sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin sun kuma kama daya, inda suka ruwaito hakan daga kodinatan cibiyar labarai ta kasa Mike Omeri.