Tsohon mataimakin Gwamnan Enugu ya mayar da albashinsa

Tsohon Mataimakin Gwmanan Enugu, Sunday Onyebuchi, da aka tsige ya mayar da albashinsa na watan Satumba, inda ya soki lamirin gwamnatin kan biyasa kudin aikin da bai yi ba.  Ya kudin a baitul malin Gwamantin Jihar, wanda aka ce an biya shi ne a matsayinsa na Mataimakin Darakata a Hukumar daukar Ma’aikata, inda ya jajice […]

Tsohon mataimakin Gwamnan Enugu ya mayar da albashinsa
Tsohon mataimakin Gwamnan Enugu ya mayar da albashinsa

Tsohon Mataimakin Gwmanan Enugu, Sunday Onyebuchi, da aka tsige ya mayar da albashinsa na watan Satumba, inda ya soki lamirin gwamnatin kan biyasa kudin aikin da bai yi ba. 

Ya kudin a baitul malin Gwamantin Jihar, wanda aka ce an biya shi ne a matsayinsa na Mataimakin Darakata a Hukumar daukar Ma’aikata, inda ya jajice kan cewa, wannan wata “rashawa ce kawai.”
Bayan da aka tsige mataimakin gwamanan, sai Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Patrick Okolo ya mayar da tsigaggen mataimakin gwamnan matsayin mataimakin darakata, a matakin albashi na 15.
A wata wasika da da Okolo ya rubuta wa Onyebuchi, a ranar 1 ga Satumbar bana, ya bayyanba cewa, an bas hi mukamin ne, bayan ya bar rike “mukamin siyasa.”
Sai dai shi Onyebuchi, ya ce, ya cika da mamaki ganin cewa, gwamnati ta biya a asusun ajiyarsa na banki, inda aka zuba masa Naira dubu 61 da 67,a amtsayin albashin watan Satumbar 2014.
Ya ce, ya daina aikin gwamnati tun daga shekarar 2007, don tsayawa takarar zabe,kuma bai taba neman a sake daukarsa aiki ba.
A wasikar day a aike wa SakatarenGwamnatin, mai dauke da kwananan watan 8 ga Oktobar 2014,mai take: Mayar da kudin kullin makirci da aka biya ni,” a cewarOnyebuchi, ind aya hada musu darasitin biyan kudi na baitul mali gwamantin jiha, inda ya yi nuni da cewa, “hanzarin bashi kudin” albashin aikin da bai yi ba, “share fagen kulla makirci ne, wand anan ba dadadewaasiri zai tonu.”
Onyebuchi y ace, a martanin da ya aike na wasikar daukarsa aiki, ranar 5 ga Satumbar 2014, ya tunatar da gwamantin jihar cewa ya ajiye aiki tun a shekarar 2007,don cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada ga dukkan mai tson tsayawa takarar zabe a karkashin kowace jam’iyyar siyasa.