Tsohon mataimakin shugaban APC ya rasu

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC a Arewa Maso Yamma, Barista Inuwa Abdulƙadir, ya rasu yana da shekarru 54 a duniya. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usumanu Danfodio, Sakkwato, bayan ya yi jinya ta takaitaccen lokaci. A lokacin rayuwarsa shi ne shugaban kwamitin zartarwar Jami’ar Jihar Sakkwato, kuma za a yi masa zana’iza […]

Tsohon mataimakin shugaban APC ya rasu

Marigayi Inuwa Abdulkadir

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC a Arewa Maso Yamma, Barista Inuwa Abdulƙadir, ya rasu yana da shekarru 54 a duniya.

Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usumanu Danfodio, Sakkwato, bayan ya yi jinya ta takaitaccen lokaci.

A lokacin rayuwarsa shi ne shugaban kwamitin zartarwar Jami’ar Jihar Sakkwato, kuma za a yi masa zana’iza ranar Litinin.

Marigayin yana cikin manyan aminan gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.