Tsohon Minista Mahmud Tukur ya rasu
Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana’atu, Mahmdu Tukur ya rasu a safiyar Juma’a.
Allah Ya yi wa tsohon Ministan Ciniki da Masana’atu, Dokta Mahmdu Tukur rasuwa a safiyar Juma’a 9 ga Afrilu, 2021.
Dokta Mahmud Tukur, shi ne Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) na farko, kuma makusanci ne ga Shugaba Muhammadu Buhari.
- Matar aure mai sana’ar tuka Keke NAPEP a Kano
- An kashe sojoji 11 a bakin aikinsu a Binuwai
- Dalibi ya yi doguwar suma bayan yi masa bulala 6,000
Iyalansa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a Abuja bayan fama da rashin lafiyar da ta sa aka garzaya da shi zuwa asibiti daga Kaduna a ranar Alhamis da dare.
“Za a kai gawarsa Yola, Jihar Adamawa domin yi masa jana’iza,” inji majiyar tamu.
A lokacin rayuwarsa, Dokta Mahmud Tukur ya taba za darakta a kamfanin Cadbury Nigeria.