Tsohon minista Tuggar ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamnan Bauchi

Tsohon ministan ya ce jihar na buƙatar nagartattun mutane da za su jagorance ta.

Tsohon minista Tuggar ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamnan Bauchi

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya; Yusuf Maitama Tuggar

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC a shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayansa a Games Village da ke Bauchi.

Tuggar, ya ce Bauchi na buƙatar nagartaccen shugabanci domin inganta rayuwar jama’a, yana mai cewa rashin kyakkyawan mulki ya hana ci gaba a jihar.

Ya ce abubuwan da ya fuskanta a siyasa a baya, ciki har da rashin nasara a zaɓe, sun ƙara masa ƙarfi da ƙuduri na yi wa jama’a hidima cikin gaskiya da jajircewa.

Tuggar, wanda ya wakilci mazaɓar Gamawa a Majalisar Wakilai a shekarar 2007, ya ce ya yi murabus daga muƙaminsa kamar yadda doka ta tanada ga masu neman takarar zaɓe.

Ya kuma ce ya dawo takarar gwamna ne domin kawo ci gaba a Bauchi, yana mai cewa har yanzu mutane da dama a jihar na fama da talauci da rashin ingantaccen ilimi da lafiya.

Ya yi alƙawarin yin shugabanci cikin adalci, kare ƙananan ƙabilu, da kuma ƙara bai wa mata da marasa ƙarfi damar shiga gwamnati.

Tuggar, ya buƙaci masu zaɓe su mara wa shugabanni masu hangen nesa da gaskiya baya, yana mai cewa ci gaba na gaskiya ba zai samu ba sai da shugabanci na gari.