Tsohon Ministan Kudi ya lashe zaben Shugaban kasa a Madagascar
Tsohon Ministan Kudi na kasar Madagascar Mista Hery Rajaonarimampianina ya lashe zaben Shugaban kasar na farko bayan juyin mulkin soja na shekarar 2009, sai dai wanda ke binsa a zaben ya ce an tafka magudi lamarin da ke nuna kasar za ta ci gaba da fama da tankiyar siyasa.Kamfanin Dillancin Labarai na Reueters ya ruwaita […]
Tsohon Ministan Kudi na kasar Madagascar Mista Hery Rajaonarimampianina ya lashe zaben Shugaban kasar na farko bayan juyin mulkin soja na shekarar 2009, sai dai wanda ke binsa a zaben ya ce an tafka magudi lamarin da ke nuna kasar za ta ci gaba da fama da tankiyar siyasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reueters ya ruwaita a ranar Juma’ar da ta gabata cewa Mista Rajaonarimampianina, da ke samun goyon bayan Shugaba mai barin gado Andry Rajoelina ya samu kashi 53 da rabi daga cikin 100 na zaben da aka gudanar a ranar 20 ga Disamban da ya gabata.
Ya kada Jean Louis Robinson, wanda ke da kashi 46 da rabi cikin 100 na kuri’un da aka kada, kuma ke neman a sake kirga kuri’un. bangaren Robinson ya mika koke-koke har 300 ga kotun zabe, wadda take da dama yanke hukunci kan sakamakon zaben na farko nan da 19 ga Janairu.
to the electoral court, which has to rule on the commission’s probisional result by January 19.
Ba a gudanar da bukukuwan murna a babban birnin kasar Antananaribo ba, inda Rajaonarimampianina ya yi faman neman goyon bayan jama’a a zagayen farko.
Rajaonarimampianina ya shaida wa manema labarai cewa, “Ina kira ga al’ummar Madagascar su jira sakamakon karshe na zaben.”
Da aka tambaye shi game da zargin magudin zabe, ya ce, “Shi (Robison) ne ya fadi haka ba jama’ar kasa ba.
Robinson ya kaurace wa wurin bayyana sakamakon zaben.
“Mun fada tuntuni akwai gagarumar magudin zabe a sassan Madagascar,” inji Elyse Razaka wanda ya taimaka wajen gudanar da kamfe din Robinson. Ya kara da cewa, “Robinson ba zai ba jama’ar umarnin su fito kan don zanga-zanga ba. Sai dai wani abu ne daban idan akwai wani yunkri da ake yi kan lamarin.”
Ana fata zaben ya kawo karshen rikicin kasar wanda ya kori masu zuba jari, kuma ya takaita masu ba da tallafi tare da jawo tafiyar hawainiya ga tattalin arzikin kasar.