Tsohon Ministan Kwadago Musa Gwadabe ya rasu

Za a yi jana’izarsa a layin Madaka da ke kan tittin Maiduguri da Kano da misalin karfe 2 na rana

Tsohon Ministan Kwadago Musa Gwadabe ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon Ministan Kwadago kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Musa Gwadabe, rasuwa

Ahaji Musa Gwadabe ya rasu ne a kafin wayewar garin ranar Laraba bayan fama da jinya yana da shekaru 87 a duniya.

Za a gudanar da jana’izarsa a gidansa da ke daura da tittin Maiduguri da Kano da misalin karfe 2 na rana.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 11 da kuma jikoki.

Daga cikin ’ya’yansa akwai Alhaji Nazifi Musa Gwadabe, wanda dan kwangila ne a Jihar Kano.

Alhaji Musa Gwadabe ya kasance minista a zaman mulkin shugaba Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2003 kuma shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Kano a zamanin marigayi Alhaji Sabo Sabo Bakin Zuwo.

Hakazalika a lokacin rayuwarsa ya kasance mamba a kwamitin amintattu a lokuta daban-daban, kuma ya ta taba zama Shugaban Gwamnatin Daraktoci na Hukumar ITF.