Tsohon Mukaddashin Gwamnan Taraba ya tashi a tutar babu

Bisa dukkan alamu tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya tashi a tutar babu, a kokarinsa na neman tsayawa takara a karkashin Jam’iyar PDP. Watan ya wuce ne aka cire shi daga kujerar mulki kuma shi ne dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar amma sai ga shi ya tashi a […]

Tsohon Mukaddashin Gwamnan Taraba ya tashi a tutar babu
Tsohon Mukaddashin Gwamnan Taraba ya tashi a tutar babu

Bisa dukkan alamu tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya tashi a tutar babu, a kokarinsa na neman tsayawa takara a karkashin Jam’iyar PDP.

Watan ya wuce ne aka cire shi daga kujerar mulki kuma shi ne dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar amma sai ga shi ya tashi a tutar babu.
Wannan ya biyo bayan wani dodoridon zaben fidda dan takarar Gwamna na jam’iyyar da aka dauke daga Jalingo fadar jihar zuwa Abuja.
A wannan zabe an tilasta wa Alhaji Garba Umar barin takarar Gwamnan, lamarin da ake zargin Shugaba Goodluck da Janar T.Y. danjuma da hannu dumu-dumu a ciki. Kuma duk ’yan takarar da ke alaka da tsohon Mukaddashin Gwamnan an hana su tsayawa a takarar fidda gwani na mukamai daban-daban.
Majiyarmu ta ce daga bisani an tilasta wa Alhaji Garba Umar karbar tikitin takarar dan Majalisar Dattawa na mazabar Taraba ta Arewa da ta kunshi kananan hukumomin Jalingo da Lau da Yorro da Zing da Ardo- Kola da kuma Karim-Lamido.
Tsohon Mukaddashin Gwamnan da mai ci yanzu Alhaji Sani Abubakar danladi garinsu daya, kuma kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu, Alhaji Sani danladi bayan ya dare kujerar mulki sai ya soma tunanin yadda zai karbe wannan tikiti domin ya yi takararb Sanata.
Majiyar ta ce Alhaji Garba Umar na zaune a gidansa da ke Abuja sai Alhaji Sani danladi ya ziyarce shi a makon jiya, inda ya fada wa Alhaji Garba cewa daga fadar Shugaban kasa ne aka turo shi wurinsa da sakon za a ba shi tikitin takarar Gwamnan saboda haka ga takarda ya sa hannu ya amimce ya bar wa Sani danladi tikitinsa na takarar Sanata.
Majiyar ta ce Alhaji Garba Umar bai yi tsammanin akwai yaudara a cikin wannan magana ba, domin Mukaddashin Gwamna Sani danladi ya fada wa Garba Umar cewa Shugaban kasar zai gana da shi a yammacin wannan rana.
Majiyar ta ce jin haka ne sai Alhaji Garba Umar ya amince da wannan magana kuma nan take ya rattaba hannu a kan takardar. Kuma a cewar majiyar lokacin da Alhaji Garba Umar ya isa kofar shiga fadar Shugaban kasa ya sha mamaki domin an shaida masa cewa ba sunnansa a cikin wadanda Shugaban kasar zai gan su a ranar kuma ba wani shiri kamar haka a fadar.
kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin tsohon Mukaddashin Gwamnan da kuma mai ci yanzu ya faskara.
Amma ya bayyana a Jihar Taraba cewa Alhaji Sani Abubakar danladi ne dan takarar Sanata na Taraba ta Arewa ba Alhaji Garba Umar ba kamar yadda yake a da ba.