Tsohon Sakataren APC ya fice a jajibirin zaben dan takarar shugaban kasa
Sanata Akpanudeodehe dai yana takun saka da Ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio
Tsohon Sakataren Riko na Jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fice daga cikinta, kasa da awa 24 da zaben fitar da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.
Sanata Akpanudeodehe shi ne Sakataren Jam’iyyar a Karkashin Kwamitin Riko da Shirya Babban Taron Jami’iyyar, wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jagoranta.
- Majalisa ta dage dawowarta daga hutu saboda taron APC
- Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Damaturu-Maiduguri
Sanarwar ficewarsa da ya sanya hannu a ranar Litinin ta nuna cewa ya yanke shawarar raba gari da APC ne bayan matsin lamba da ya samu daga magoya baya da kuma mukarrabansa na siyasa.
Sanata Akpanudeodehe dai yana takun saka da Ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, game da shugabancin APC a jiharsu ta Akwa Ibom.
Hakan ya haddasa rabuwar kai tare da samar da bangarori biyu, amma kuma, uwar jam’iyyar ta san da zaban bangaren Akpabipo.