Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Aminu Saleh ya rasu
Allah Ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, wato Alhaji Aminu Saleh (Wamban Katagum) rasuwa bayan ya yi gajeriyar jinya a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke garin Azare a Jihar Bauchi. Marigayin wanda ya rasu a shekaranjiya Laraba yana da shekara 87 ya rike mukamai da dama a gwamnatin […]
Allah Ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, wato Alhaji Aminu Saleh (Wamban Katagum) rasuwa bayan ya yi gajeriyar jinya a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke garin Azare a Jihar Bauchi.
Marigayin wanda ya rasu a shekaranjiya Laraba yana da shekara 87 ya rike mukamai da dama a gwamnatin jiha da ta tarayya tun daga Jamhuriyya ta daya har zuwa zamanin Shugaba Shehu Shagari da gwamnatin rikon kwarya ta Shonekan da gwamnatin marigayi Abacha da ta Obasanjo.
An haifi marigayi Aminu Saleh ne a 1933 a garin Azare da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi, kuma ya halarci makarantar elemantare ta Azare daga 1941 zuwa 1944 sai makarantar midil ta Bauchi daga 1944 zuwa 1949.
Alhaji Aminu Saleh ya halarci Kwalejin Koyar da Aikin Akawu da ke Zariya daga 1950 zuwa 1951, sai Cibiyar Nazarin Harkokin Mulki inda ya yi diploma a aikin akanta daga 1956 zuwa 1957. Ya yi karatun yamma na neman digiri daga jami’ar Legas daga 1963 zuwa 1967, sannan ya halarci kwas din babban digiri kan shugabanci a Jami’ar Wisconsin da ke Amurka.
Alhaji Aminu Saleh ya fara aiki ne a Hukumar En’e ta Katagum a 1949, inda ya zama Ma’ajin En’e ta Katagum a 1957 kafin ya koma aiki da Gwamnatin Tarayya a 1962. Ya yi aiki a karkashin Dokta Pius Okigbo Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Tattalin Arziki ga Firayi Ministan Najeriya a wancan lokaci.
Sauran mukaman da ya rike sun hada da Ministan Kudi da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Tsaro da Ministan Kasuwanci da Shugaban Ma’aikata na Tarayya da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugaban Kwamitin Musabakar Alkur’ani n++a kasa. Kuma ya rike mukamin Mataimakin Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ta sadarwa da ta aikin gona. Sannan ya zama Babban Sakatare a ma’aikatun sadarwa da na kasuwanci da na tsaro kafin a nada shi Ministan Masana’antu a 1993, sai Ministan Kudi daga nan ya zama Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Ma’aikata na kasa kafin ya yi ritaya daga aiki.
Ya kasance wakili a hukumomi da kwamitoci da dama, sannan ya samu lambar yabo ta kasa ta GCON a zamanin gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar sai digirin girmamawa na dokta daga Jami’ar Abubakar Tafawa balewa, sannan Shugaba Umaru ’Yar’aduwa ya karrama shi da lambar yabo ta kasa ta CFR.
An yi jana’izarsa a jiya Alhamis a garin Azare kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai Alhaji Kabir Aminu Saleh na Ma’aikatar Tama da karafa ta Tarayya da Alhaji Tijjani Aminu Saleh da kuma Alhaji Sagir Aminu Saleh, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi a zangon Gwamna Yuguda na karshe.