Tsohon Sakataren PDP Ojo Madueke ya rasu
Tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP ta kasa kuma tsohon Ministan Harkokin kasashen Wajen Najeriya, Cif Ojo Madueke ya rasu.Wasu majiyoyi sun ce Cif Madueke ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja, a shekaranjiya Laraba da almuru, bayan ya kamu da rashin lafiya a cikin jirgin da ya dauko shi daga Dubai zuwa Abuja lokacin […]

Tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP ta kasa kuma tsohon Ministan Harkokin kasashen Wajen Najeriya, Cif Ojo Madueke ya rasu.
Wasu majiyoyi sun ce Cif Madueke ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja, a shekaranjiya Laraba da almuru, bayan ya kamu da rashin lafiya a cikin jirgin da ya dauko shi daga Dubai zuwa Abuja lokacin da ya baro Amurka, kuma da saukar jirgin aka garzaya da shi asibiti, inda ya rasu jim kadan da kai shi asibitin.
Cif Madueke ya rike mukamai da dama a ciki da wajen Najeriya, inda tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya nada shi Minsitan Al’adu da Yawon Bude Ido a 1999, yayin da ya zama Ministan Sufuri a shekarar 2001, kuma a lokacin ne ya rika shelar ’yan Najeriya su koma hawan kekuna saboda shi mai sha’awar hawa keke ne, lamarin da ya jawo masa shan suka daga jama’a wadanda suke cewa kamata ya yi a gyara hanyoyi ba maganar komawa hawa kekuna ba.
Cif Madueke wanda ya rasu yana da shekara 71 an haife shi ne a ranar 6 ga Mayun 1945 a Jihar Abiya.