Tsohon Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu
Qatar, wadda ta samu ’yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1971, na ƙarƙashin mulkin gidan sarautar Al Thani tun daga tsakiyar ƙarni na 19.
Gwamnatin Qatar ta sanar da rasuwar tsohon Sarkin ƙasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, wanda ya jagoranci ƙasar daga shekarar 1995 zuwa 2013.
A cikin wata sanarwa da Fadar Sarkin Qatar ta wallafa, gwamnatin ta bayyana rasuwar Sheikh Hamad a matsayin babban rashi ga ƙasar, tana mai yi masa addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.
- INEC ta ƙara wa’adin karɓar sunayen ’yan takara na Zaɓen 2027
- Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz har sai abin da hali ya yi
Sheikh Hamad wanda ya rasu yana da shekaru 74, yana daga cikin manyan jagororin da suka taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin Qatar zuwa ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziki da tasiri a duniya.
Ya hau mulki ne a watan Yunin 1995, bayan ya hamɓarar da mahaifinsa a wani juyin mulki da aka yi ba tare da zubar da jini ba, yayin da mahaifin nasa ya yi balaguto zuwa ƙetare.
A lokacin da ya karɓi mulki, Qatar ƙaramar ƙasa ce mai ƙarancin tasiri da ƙarancin kuɗaɗe.
Sai dai ya yi amfani da ɗimbin arzikin iskar gas da ƙasar ke da shi wajen bunƙasa tattalin arzikinta, inda ta zama ɗaya daga cikin manyan masu samarwa da fitar da iskar gas mai ruwa (LNG) a duniya.
A zamaninsa ne aka kafa tashar talabijin ta Al Jazeera a shekarar 1996, wadda daga baya ta zama ɗaya daga cikin manyan kafafen yaɗa labarai masu tasiri a duniya.
Haka kuma, ya kafa Asusun Zuba Jari na Qatar (Qatar Investment Authority), wanda ya zuba biliyoyin daloli a manyan kamfanoni da kadarori a ƙasashe daban-daban, ciki har da kamfanin ƙera motoci na Volkswagen, shagon Harrods da ke Landan da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain.
A shekarar 2010, a lokacin mulkinsa ne Qatar ta samu damar karɓar bakuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2022, duk da cewa an yi ta zarge-zargen cin hanci da kuma suka kan yadda ake mu’amala da ma’aikatan ƙasashen waje.
A zamaninsa ne kuma Qatar ta fara bayar da tallafin kuɗi na ɗaruruwan miliyoyin daloli ga Zirin Gaza, musamman wajen gina hanyoyi da sauran ayyukan raya ƙasa. Har ila yau, wani asibiti da ke Gaza City na ɗauke da sunansa.
A watan Yunin 2013, Sheikh Hamad ya ba mutane mamaki bayan ya sauka daga mulki da kansa, inda ya miƙa ragamar shugabanci ga ɗansa, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
Wannan ya kasance ɗaya daga cikin lokuta kaɗan da aka ga shugaban ƙasar Larabawa ya sauka daga mulki bisa ra’ayin ransa.
Qatar, wadda ta samu ’yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1971, na ƙarƙashin mulkin gidan sarautar Al Thani tun daga tsakiyar ƙarni na 19.
Yawan al’ummar ƙasar ya kai kusan miliyan uku, mafi yawansu kuwa ma’aikata ne daga ƙasashen waje.