Tsohon Shugaba George Bush ya shiga sahun masu zane

A ranar Asabar da ta gabata ne tsohon Shugaban Amurka George W. Bush, wanda ya shiga sahun masu zane, ya baje kolin wasu zane da ya yi da hannunsa, na fuskokin wasu shugabannin kasashen duniya 24, a wani gidan tarihi da ke birnin Dallas.Tsohon Shugaba George Bush ya fara aikin zanen ne shekaru uku bayan […]

Tsohon Shugaba George Bush ya shiga sahun masu zane

A ranar Asabar da ta gabata ne tsohon Shugaban Amurka George W. Bush, wanda ya shiga sahun masu zane, ya baje kolin wasu zane da ya yi da hannunsa, na fuskokin wasu shugabannin kasashen duniya 24, a wani gidan tarihi da ke birnin Dallas.
Tsohon Shugaba George Bush ya fara aikin zanen ne shekaru uku bayan saukarsa daga karagar mulki.
Cikin wadanda ya zana har da tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Kufour.  Haka nan akwai shugabar kasar Laberiya, Madam Ellen Johnson Sirleaf da dai wasu sauran shugabannin.
Daga cikin zanen-zanen da aka baje kolin nasu, akwai nashi na kansa da na mahaifinsa, wanda yake shi ma tsohon shugaban Amurka ne wato George H. W. Bush. Sai kuma zanen wasu shugabannin kamar su: Shugaban kasar Rasha bladimir Putin da Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai da Shugaban kasar Indiya Manmohan Singh da tsohon shugaban Pakistan Perbez Musharraf da dai sauransu.
A jawabinsa  lokacin bude bikin baje kolin, tsohon Shugaba George Bush ya bayyana yadda aikin ya dauke shi shekaru biyu da kuma yadda ya zabi shugabannin kasashe 24 cikin dimbin shugabannin da ya yi aiki tare da su a zamanin mulkinsa, wanda ya fara daga shekarar 2001 zuwa 2009.
A karshe ya ce aikin ya ba shi damar siffanta abokansa da kuma wadanda yake wa kallon abokan gabarsa da siffar da ya ga dama saboda, a cewarsa, ya san su sosai cikin shekaru takwas da ya kwashe yana mulkar kasar ta Amurka.
Sauran wadanda ya zana sun hada da: Yarima mai Jiran Gadon Sarautar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Muhammad bin Zayed da  Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel  da Jagoran yankin Tibet, Dalai Lama da tsohon Firayiministan Birtaniya Tony Blair da kuma tsohon Firayiministan kasar Italiya Silbio Berlusconi da dai sauransu.