Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya koma gidan yari

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya koma gidan yari a wani sabon juyi a hukuncin da aka yanke masa kan raina kotu.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya koma gidan yari

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma. (Hoto: GUILLEM SARTORIO / AFP)

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya koma gidan yari a wani sabon juyi a hukuncin da aka yanke masa kan raina kotu.

Wannan wani sabon juyin waina ne a kan daurin da aka yi wa tsohon shugaban kasar mai shekara 81 kan laifin raina kotu.

Mista Zuma wanda kotu ta umarci ya koma kurkuku, ya isa gidan yarin Estcourt ne da misalin karfe 6 na safe “aka shige da shi ciki”, in ji jami’an gidan yarin.

Sai dai kuma ba a fi sa’a guda ba, aka sake shi, a karkashin tsarin rage cunkoso a gidajen yari, kamar yadda kwamishinan gidajen yarin kasar, Makgothi Thobakgale, ya sanar.

Ya ce, “Da zuwansa, ab tantance shi,… daga bisani aka sallame shi,” kamar yadda Thobakgale ya sanar da manema labarai a birnin Pretoria.

A watan yuni aka yanke wa Jacob Zuma hukuncin daurin wata 15 a gidan yari saboda kin zuwa ya ba da shaida a gaban  kwamitin binciken zargin rashawa da fifita mukarrabansa a lokacin da yake shugaban kasa.

Bayan wata biyu aka sake shi saboda rashin lafiyarsa, bayan da aka kwantar da shi a asibiti kafin a ba shi damar komawa gida a matsayin wani bangare na wa’adinsa na zaman wakafi.Daure shi a watan Yulin 2021 ya jawo boren da aka kashe mutum 350 a Afirka ta Kudu, adadi mafi yawa tun bayan komawar kasar kan tafarkin dimokuradiyya.A watan Nuwambar bara kotun daukaka kara ta gano cewa sakin nasa ba bisa ka’ida ba ne, saboda haka ta umarce shi da komawa gidan yarin na Estcourt da ke lardin KwaZulu-Natal.

Hukumar gidajen yarin kasar ta daukaka kara, amma kotu ta yi watsi da bukatar a watan Yuli da ya gabata, ta kuma umarce shi ya koma gidan yarin a ranar Juma’a.

Sai dai zuwansa gidan yarin ke da wuya kuma ya ci gajiyar tsarin afuwa ga daurarru marasa hadari, na Shugaban Cyril Ramaphosa.

Minisan Shari’a Ronald Lamola ya sanar cewa fursunoni 24,000 ne za su ci gajiar tsarin.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu