Tsohon Shugaban Alkalan Najeriya Ibrahim Tanko ya rasu
Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Alkalai Na Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko, rasuwa.
Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad
Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, rasuwa.
Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, ya rasu yana da shekara 71, kamar yadda Gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a ranar Talata da safe.
Kungiyar Dalibai Musulmi a Fannin Aikin Lauya ta Najeriya (NAMLAS) ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.
- Kasuwar Katakon Gombe ta yi gobara na 2 cikin wata ɗaya
- Buhari ya yarda cewa ina neman kashe shi —Aisha
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana rasuwar Mai Shari’a Tanko Mohammed a matsayin “babban rashi ga fannin aikin shari’a a Najeriya, daukacin aikin shari’ar, da al’ummar Musulmi baki daya.”
Hakazalika Gwamantin Jihar Bauchi ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, tana mai addu’ar Allah Ya yi masa rahama, Ya kuma ba wa iyalansa hakurin jure wannan rashi.