Tsohon shugaban Bankin Access Herbert Wigwe ya mutu a haɗarin jirgin sama

Jirgin ya yi hatsari ɗauke da Herbert Wigwe da kuma matarsa da ɗansa.

Tsohon shugaban Bankin Access Herbert Wigwe ya mutu a haɗarin jirgin sama

Tsohon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Access Holdings, Herbert Wigwe ya rasu a haɗarin jirgin sama a Amurka.

Bayanai sun ce attajirin yana cikin wani jirgi mai saukar ungulu ne tare da matarsa, dansa da wasu fasinjoji uku lokacin da tsautsayin ya faru a yankin California.

Jaridar New York Times ta tabbatar da faruwar lamarin ba tare da fitar da sunayen fasinjojin da ke cikin jirgin ba.

Wata majiya mai tushe daga bangaren bankin a Najeriya ta bayyana cewa Herbert Wigwe, babban jami’in gudanarwa na kungiyar Access Holdings Plc, ya yi hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu a Amurka, ranar Juma’a, da wasu mutane biyar a California.

Jirgin ya faɗo kusa da wani gari mai iyaka tsakanin Nevada da California a daren Juma’a.

An kuma ruwaito cewa Herbert Wigwe na kan hanyar zuwa Las Vegas don kallon Super Bowl, wasan zakarun lig na shekara-shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Ƙasa (NFL) ta Amurka.

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu