Tsohon shugaban Gidan Rediyon Kano, Adamu Getso ya rasu
Kafin rasuwar marigayin, ya kuma riƙe muƙamin shugaban gidan talabijin na CTV/ARTV Kano.
Yadda aka gudanar da jana’izar Marigayi Adamu Ibrahim Getso tsohon shugaban gidan Radio Kano a garin Getso.
Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon Shugaban Gidan Rediyon Kano, Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya riga mu gidan gaskiya.
Bayanai sun ce marigayin wanda kuma shi ne Galadiman Getso ya rasu ne a yammacin Asabar a gidansa da ke Ƙofar Fada a garin Getso da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
- ’Yan sanda sun kama mutum 5 da kayan layin dogo da aka sato a Yobe
- Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a Gombe
Kafin rasuwar marigayin, ya kuma riƙe muƙamin shugaban gidan talabijin na CTV/ARTV Kano.
An gudanar da jana’izarsa da safiyar wannan Lahadin a gidansa da ke garin Getso, inda ’yan uwa da abokan arziki da masu alhini suka halarta domin yi masa bankwana na ƙarshe.
Rasuwarsa ta girgiza masu ruwa da tsaki a kafafen yaɗa labarai a Kano da ma Najeriya baki ɗaya, inda ake ci gaba da bayyana alhini tare da tuna gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin aikin jarida.