Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
Da farko ‘yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansarsa.

Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga.
An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari.
- Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250
- Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta
Maharan sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sako shi.
Sai dai bayan tattaunawa, an biya kuɗin fansa, wanda ya kai ga sakinsa.
A halin yanzu, likitoci na kula da shi a wani asibiti da ba a bayyana ba sunansa ba.
A lokacin kai harin, sama da ’yan bindiga 100 ne suka afka gidansa, suka yi awon gaba da shi da wasu mazauna yankin.
Wasu mutum biyu sun samu raunuka yayin harin, yayin da wani daga cikin ’yan bindigar ya harbi ɗan uwansa bisa kuskure, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Har yanzu, rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan sakin tsohon shugaban NYSC ɗin ba.
Satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaro a Jihar Katsina da sauran sassan Najeriya.
Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro na fuskantar matsin lamba wajen shawo kan wannan matsala.