Tsohon Shugaban Iran ya soki cire jikan Khomeini daga shiga takara
Tsohon Shugaban Iran Akbar Hashemi Rafasanjani ya soki kwamitin ba ’yan takara damar tsayawa a zabe kan yadda ya cire jikan marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini jagoran kafa Jamhuriyyar Musulunci ta Iran daga tsayawa takara.Kamfanin Dillancin Labarai na AFP a Tehran babban birnin Iran ya ruwaito cewa a ranar Litinin Hashemi Rafsanjani ya soki kwamitin inda […]
Tsohon Shugaban Iran Akbar Hashemi Rafasanjani ya soki kwamitin ba ’yan takara damar tsayawa a zabe kan yadda ya cire jikan marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini jagoran kafa Jamhuriyyar Musulunci ta Iran daga tsayawa takara.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP a Tehran babban birnin Iran ya ruwaito cewa a ranar Litinin Hashemi Rafsanjani ya soki kwamitin inda ya ce: “Wa ya ba ku hakkin yin wannan hukunci? Wa ya ba ku damar ku tsaya ku yi hudubar Juma’a da jawabi a talabijin din kasa?” yana magana kan hana Hassan Khomeini tsayawa takarar shiga Majalisar kwararru mai fadi-a-ji a Iran.
“Allah Ya gafarta muku,” Kamfanin Dillancin Labarai na Iran (IRNA) ya ruwaito Rafasanjani jigo a siyasar Iran da ya shugabanci kasar sau biyu yana fadi.
Ya kara da cewa: ‘Ba don Imam (Ruhollah) Khomeini ba, ba daya daga cikin mutanen nan (da ke cikin kwamitin) da zai kai wannan matsayi.”
Hassan Khomeini, wanda malami ne mai shekara 43 da yake da alaka da masu ra’ayin sauyi a Iran, ya fadi a ranar Juma’a cewa zai daukaka kara kan hana shi tsayawa takarar.
Yana daga cikin daruruwan mutanen da aka cire sunayensu daga shiga zaben majalisar da za a gudanar a watan nan, majalisar da ita ke sanya ido kan ayyukan shugaban addini na Iran kuma wakilinta ke iya maye gurbinsa.
Majalisar Kare Juyin Juya-Hali wadda masu tsattsauran ra’ayi suka fi rinjaye a cikinta c eke yanke shawara kan wadanda za su tsaya takara, kuma ta ce mutum 166 daga cikin mutum 800 masu son tsayawa takarar ne kawai ta amince musu.
Hassan Khomeini, wanda bai samu zuwa jarrabawar tantance ’yan takarar ba, ya ce an riga an zabi wadanda za su tsaya takarar tun ma ba a yi jarrabawar ba.
Wakilan majalisar 88 da za a zaba da Rafsanjani wakili ne a cikinta kuma yake son sake tsayawa takara, zai gudana ne a ranar 26 ga Fabrairun nan, rana guda da zaben majalisar dokokin kasar.
Dukkan majalisun biyu masu tsattsauran ra’ayi ne suke da rinjaye.
Majlisar Kare Juyin Juya-Halin ta fadi a makon jiya cewa kashi 60 cikin 100 na masu son tsayawa takarar majalisar aka yi waje da sunayensu. Kuma kashi daya kacal ne na masu ra’ayin sauyi aka amince da sunayensu.
Shugaban Iran Hassan Rouhani mai sassaucin ra’ayi ya so ya samu karin wakilai daga bangaren masu sassaucin ra’ayi domin ya samu damar gudanar da harkokin siyasa da rayuwar jama’a cikin sauki.