Tsohon Shugaban Jama’atu Nasril Islam ya rasu

Ɗaya daga cikin fitattun shugabannin addini kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Alhaji Jafaru Makarfi ya riga mu gidan gaskiya. Garkuwan Zazzau, Alhaji Suleiman Abdulkadir wanda ya fitar da sanarwa a madadin iyalansa, ya ce Alhaji Makarfi ya rasu ne a ranar Asabar da daddare a Jihar Kaduna bayan shafe shekaru 93 a doron ƙasa. Dokar sake […]

Tsohon Shugaban Jama’atu Nasril Islam ya rasu

Ɗaya daga cikin fitattun shugabannin addini kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Alhaji Jafaru Makarfi ya riga mu gidan gaskiya.

Garkuwan Zazzau, Alhaji Suleiman Abdulkadir wanda ya fitar da sanarwa a madadin iyalansa, ya ce Alhaji Makarfi ya rasu ne a ranar Asabar da daddare a Jihar Kaduna bayan shafe shekaru 93 a doron ƙasa.

Ya bayyana cewa za a yi jana’izar mamacin a Masallacin Sultan Bello da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadin nan.

Marigayi Makarfi wanda sanannen mutum ne a cikin al’ummar Musulmi a Najeriya, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna.

Haka kuma, marigayin ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishina a tsohuwar Jihar Kaduna.

Kazalika, Alhaji Makarfi ya yi fice a Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) inda ya shafe tsawon shekaru 40 yana aikin da ya soma a shekarar 1950.

Alhaji Makarfi ya rasu ya bar ’ya’ya shida kamar yadda sanarwar da Garkuwan Zazzau ya fitar ta bayyana.

 

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe