Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu
Ana sa ran gudanar da Sallah Jana’izar Farfesa AbdulGaniyu Ambali bayan Sallar La’asar a gidansa da ke Ilori
Farfesa AbdulGaniyu Ambali
Allah Ya yi wa Shugaban Jami’ar Ilolin, Farfesa AbdulGaniyu Ambali, rasu a safiyar nan ta Asabar.
Farfesa Abdulganiya ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya, a gidansa da ke rukunkin gidaje na Oloje Estate da ke Ilori, fadar Gwamnatin Jihar Kwara.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Jami’ar, Kunle Akogun, ta bayyana cewa ana sa ran gudanar da Sallah Janaza a gidan mamacin bayan Sallar La’asar.
Hukumomin Jami’ar Ilorin sun sanar da cewa Farfesa AbdulGaniyu ya rasu yana da shekaru 68.
A sakon ta’aziyyarsa, Shugaban Jami’ar Ilorin Farfesa Wahab Olasupo Egbewole, SAN, ya bayyana rasuwar Farfesa AbdulGaniyu a matsayin “Babban rashi ga Jami’ar Ilori da Jami’ar Jihar Kwara, inda halin yanzu mamacin ya kasance Uban Jami’a,” tun bayan saukansa daga matsayin Shugaban Jami’ar Ilori.
Farfesa AbdulGaniyu wanda malamin fannin aikin likitan dabbobi ne, ya kasance Shugaban Jami’ar Ilorin na 9, daga shekarar 2012 zuwa 2017.