Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Ɗan siyasar ya rasu a Jihar Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Allah Ya yi wa Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙaramar Hukumar Gombe, Alhaji Idris Bello, wanda aka fi sani da Alhaji Yaro na Gambo Isari, rasuwa.

Alhaji Yaro, ya rasu ne a daren ranar Asabar, a Kano bayan ya sha fama da doguwar jinya.

An yi jana’izarsa da misalin karfe 1 na rana a Babban Masallacin Juma’a na Izala da ke Bolari.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi wa iyalansa, jam’iyyar PDP, da al’ummar unguwar Jekadafari ta’aziyya kan rasuwar marigayn.

A wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labaran Gidan Gwamnatin Jihar, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Inuwa ya ce Alhaji Yaro fitaccen ɗan siyasa ne mai ƙwazo, kuma mutuwarsa ta bar gibi mai wahalar cikewa.

Gwamnan, ya yi addu’ar Allah ya jikan sa, ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe