Tsohon Shugaban Kamfanin Jaridar New Nigeria, Tukur Usman, ya rasu
Allah Ya yi wa tsohon Manajan-Daraktan kamfanin Jaridar New Nigeria, Tukur Usman, rasuwa.
Allah Ya yi wa tsohon Shugaban kamfanin New Nigeria da ke wallafa jaridun Gaskiya Ta Fi Kwabo da kuma New Nigeria, Tukur Usman, rasuwa.
Ya rasu ne bayan fama da jinya a Asibitn Garkuwa da ke Kaduna, ya bar mata biyu da ’ya’ya 16, kuma za a yi jana’izarsa a Masallacin Misbahu da ke Unguwar Rimi Kaduna, bayan Sallar Juma’a.
Kafin rasuwarsa Alhaji Tukur Usman, shi ne babban masahwarci na farko a sashin labarai na kamfanin FUZA Communications, da ke wallafa jaridar ‘Desert Herald’, a Jihar Kaduna.
Da yake tabbatar da rasuwar a safiyar Juma’a cikin wata sanarwa, Shugaban kamfanin Tukur Mamu, ne ya ce “Ba za mu gushe ba wajen tunawa da hidimarsa ga kasa, da duniyar aikin jarida ma baki daya.
“A madadin kamfaninmu na FUZA, ina amika ta’aziyata ga iyalansa da sauran ’yan uwa da abokan arziki.
“Muna fatan Allah Ya karbi shahadarsa, Ya kuma sanya shi a Aljanna.
Kafin rasuwarsa dai shi ne babban masahwarci a sashin labarai na farko, a kamfanin jaridar ‘Desert Herald’, wacce ake wallafawa a Jihar Kaduna.
Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, ne ya bayyana rasuwar margayin a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Juma’a.
“Ba za mu gushe ba wajen tunawa da hidimarsa ga kasa, da duniyar aikin jarida ma baki daya.
“A madadin kamfaninmu na FUZA, ina amika ta’aziyata ga iyalansa da sauran ’yan uwa da abokan arziki.
“Muna fatan Allah Ya karbi shahadarsa, Ya kuma sanya shi a Aljanna.
Za dai a yi jana`izarsa a masallacin Misbahu da ke Unguwar Rimi baya sallar Juma`a.