Tsohon Shugaban karamar Kukumar Lere ya koma APC
Tsohon shugaban riko na karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Kabiru Tahir Malali ya fice daga Jam’iyyar PDP tare da daruruwan magoya bayansa ya koma Jam’iyyar APC. Da yake jawabi a wajen taron da aka shirya don karbarsa a garin Unguwar Bawa, Alhaji Kabiru Tahir Malali ya ce a matsayinsa na wanda aka […]
Tsohon shugaban riko na karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Kabiru Tahir Malali ya fice daga Jam’iyyar PDP tare da daruruwan magoya bayansa ya koma Jam’iyyar APC.
Da yake jawabi a wajen taron da aka shirya don karbarsa a garin Unguwar Bawa, Alhaji Kabiru Tahir Malali ya ce a matsayinsa na wanda aka kafa PDP da shi a karamar hukumar da aka ba shi shugabancin rikon karamar hukuma, kuma aka fahimci ya yi ayyukan taimakon al’umma, sai aka lashi takobin raunata shi.
Ya ce an wayi gari ba a neman shawararsa, ana ganin koda shi ko babu ni za a samu nasara. “Saboda na yi abubuwan da suka saba musu, wannan ne dalilin da ya sanya na fice daga
Jam’iyyar PDP na dawo Jam’iyyar APC inda nake ganin akwai adalci,” inji shi.
Ya ce ya dawo APC tare da dukkan magoya bayansa daga mazabu 11 da ke karamar hukumar, kuma za su yi iyakar kokarinsu su ga APC ta samu nasarar ta kafa gwamnati a karamar hukumar da Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.
A jawabin shugaban Jam’iyyar APC na mazabar Sabon Birni, Yunusa Muhammad Unguwar Kura ya nuna matukar farin cikinsu da wannan kamu da suka yi.
Ya ce babu shakka wannan nasara ta nuna cewa Jam’iyyar APC ta gama mamaye karamar Hukumar Lere. Kuma ya nuna cewa jam’iyyar ce za ta yi nasara a karamar hukumar.
To amma a zantawarsa da wakilinmu, shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Alhaji Tasi’u Bala Agaji ya bukaci tsohon shugaban ya tattaro dukkan kayayyakin Jam’iyyar PDP
da ya samu ya dawo mata da su.
Ya ce PDP ta ba shi shugabancin riko na karamar hukumar ya yi gida da mota ya tafi aikin Hajji, don haka idan har PDP tana da laifi a wurinsa, ya tattaro wadannan kayayyaki da ya samu ya dawo mata da su.
Ya ce wannan ficewa da ya yi daga PDP babu wani tasiri da zai yi kan jam’iyyar.