Tsohon Shugaban Kasa, Ernest Shonekan, ya rasu
Ya rasu a Legas, yana da shekara 85.
Tsohon Shugaban Kasa na rikon kwarya, marigayi Cif Ernest Shonekan
Tsohon Shugaban Najeriya na rikon kwarya, Cif Ernest Shonekan, ya rasu.
Ya rasu ranar Talata a Legas yana da shekara 85.
- Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami na biyu a mako guda
- Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami na biyu a mako guda
Marigayin dai ya shugabanci Najeriya ne a matsayin Shugaban Kasa na rikon kwarya tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.
Tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ne ya hambarar da gwamnatinsa yayin wani juyin mulki.