Tsohon Shugaban Kasa IBB tsohon saurayina ne —Ummi Zee-zee
Ummi Zee-zee ta ce ta yi soyayya da tshohon Shugaban Kasa Babangida.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zee-zee, ta tabbatar da rade-radin da ke cewa ta yi soyayya da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida.
Ummi Zee-zee ta tabbatar da hakan ne a hirarta da Aminiya, inda ta ce amma yanzu ta rabu da IBB —tsohon masoyin nata.
- Yadda na fara nakuda, na haihu a cikin jirgi
- ’Yan bindiga sun yi wa matar aure fyaden gandu
- An cafke shugaban ’yan bindigar Neja
“Tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida tsohon saurayina ne amma yanzu ba ma tare.
“Duk da haka, yanzu mu abokan juna ne kuma muna mutunta juna. A halin yanzu kuma ina da saurayi wanda baya harkar nishadi da kuma muna shirin yin aure in Allah Ya harda,” inji ta.
Babangida, wanda ake wa lakabi da IBB, shi ne Shugaban Kasar Najeriya na mulkin soji daga 1985 zuwa 1993.
Matarsa, Maryam Babangida, ta rasu a shekarar 2009 kuma tun lokacin bai sake yin aure ba.
Kawo yanzu dai masu magana da yawun IBB ba su mai da martani ba game da ikirarin na Ummi Zee-zee cewa shi tsohon saurayinta ne.
Maganar ta Zee-zee ta zo ne watanni kadan bayan wasu mata sun fito sun yi ikirarin yin soyayya da Ali Dangote, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka.