Tsohon Shugaban Kasar Peru ya kashe kansa

Tsohon Shugaban Kasar Peru da ke Kudancin Amurka, Mista Alan Garcia ya bindige kansa, bayan wani samame da ’yan sandan kasar suka kai gidansa  da ke babban birnin kasar Lima dalilin zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa na biliyoyin Dalar Amurka. Da yake tabbatar da faruwar al’amarin a shafinsa na Twitter Shugaban […]

Tsohon Shugaban Kasar Peru ya kashe kansa

Faruk Tahir Maigari

Tsohon Shugaban Kasar Peru da ke Kudancin Amurka, Mista Alan Garcia ya bindige kansa, bayan wani samame da ’yan sandan kasar suka kai gidansa  da ke babban birnin kasar Lima dalilin zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa na biliyoyin Dalar Amurka.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin a shafinsa na Twitter Shugaban Kasar mai ci Mista Martin Bizcarra, ya ce “Na kadu matuka kuma tuni na mika ta’aziyata zuwa ga iyalansa da kuma masoyansa.”

Tun farko Lauyan tsohon Shugaban Kasar ya sanar da manema labarai cewa wanda yake karewa Mista Alan, ya dauki matakin hallaka kansa ne a lokacin da jami’an tsaro suka kai samame gidansa da ke babban birnin kasar.

Ministan cikin gida Carlos Moran ya ce ya samu labarin ne daga wajen ’yan sanda cewa a lokacin da suka isa gidan ya shaida musu cewa zai kira lauyansa amma sai suka ji karar bindiga.

Tsohon Shugaban  ya rasu yana da shekara 69 wanda yake fuskantar tuhumar karbar rashawa daga wani kamfanin kasar Brazil a lokacin da yake mulki a tsakanin  shekarar 2006 zuwa 2011.

Kafin tabbatar da mutuwarsa Ministan Lafiya na kasar, Zulem Tomas ya shaida wa manema labarai cewa tsohon Shugaban yana cikin mummunan yanayi. Ya ce kimanin likitoci 26 ne suke tsaye a kansa a kokarin ceto rayuwarsa.

Mista Garcia ya mulki kasar sau biyu daga 1985 zuwa 1990 sai kuma shekarar 2006 zuwa 2011. Yana daga cikin sha hararrun ’yan siyasa a kasar ta  Peru. Yaki amincewa da zargin da ake yi masa inda ya danganta tuhumar tasa da siyasa. A bara ne ya nemi mafakar siyasa a kasar Uruguay inda hakar tasa b ata cimma ruwa ba.

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara

Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama

Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano