Tsohon shugaban kasar Sudan Al-Dahab ya rasu
Tsohon shugaban kasar Sudan Abdulrahman Al-Dahab ya rasu a yau Alhamis. Ya rasu ne a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya kamar yadda kafar sadarwar tibi ta Al Arabiya ta sanar. Kafar sadarwar dai ba ta yi wani cikakken bayani game da rasuwar Al-Daha ba, mai shekaru 83 wanda yake shugaban kasar Sudan na biyar. Al-Dahab […]
Tsohon shugaban kasar Sudan Abdulrahman Al-Dahab ya rasu a yau Alhamis. Ya rasu ne a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya kamar yadda kafar sadarwar tibi ta Al Arabiya ta sanar.
Kafar sadarwar dai ba ta yi wani cikakken bayani game da rasuwar Al-Daha ba, mai shekaru 83 wanda yake shugaban kasar Sudan na biyar.
Al-Dahab dai tsohon jami’in soja ne da ya shugabanci Sudan daga ranar 6 ga Afrilu 1985 zuwa ranar 6 ga watan Mayu 1986 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.