Tsohon Shugaban kungiyar direbobi na Jihar Oyo ya shiga hannu

Rundunar  ’yan sandar  Jihar  Legas  ta kama  tsohon Shugaban kungiyar Direbobi ta NURTW a jihar Oyo, Alhaji Mukaila  Lamidi,  wanda  aka fi  sani da  suna Audiliary, rundunar  ta kame  shi  ne  bayan da wani  dillalin makamai  ba  bisa  ka’ida  ba, ya shiga hannunta,  wanda  ya ce  shugaban  na NURTW na  cikin  sahun masu  saye  daga  […]

Tsohon Shugaban kungiyar direbobi na Jihar Oyo ya shiga hannu
Tsohon Shugaban kungiyar direbobi na Jihar Oyo ya shiga hannu

Rundunar  ’yan sandar  Jihar  Legas  ta kama  tsohon Shugaban kungiyar Direbobi ta NURTW a jihar Oyo, Alhaji Mukaila  Lamidi,  wanda  aka fi  sani da  suna Audiliary, rundunar  ta kame  shi  ne  bayan da wani  dillalin makamai  ba  bisa  ka’ida  ba, ya shiga hannunta,  wanda  ya ce  shugaban  na NURTW na  cikin  sahun masu  saye  daga  hannunsa,  kuma  ya sayar  masa  da  bindigogi  biyu, babba da karama,samfurin AK47 da 9MM da 9MMdubu 360.
Da  aka  gabatar  da shi  gaban  manema  labarai  domin karyata  ko  gaskata  sayen  wadannan bindigogi, tsohon shugaban kungiyar  direbobin, ya ce  ba shakka  ya sayi bindigogi,  kuma  ba  ya saya  ne da niyyar  aikata  ayyukan  assha  da su  ba ne, sai domin ya kare  kansa.
Ya ce  wani abokinsa  ne ya gabatar da mai  sayar  da  wadannan bindigogin  gare  shi,  domin ya fada  cewa  shekaru  uku da suka  gabata  wasu mutane  sun taba  shiga  gidansa  da  niyyar  kashe shi,  amma  ba su  kashe  shi ba, sai  suka  kashe  babban dansa,  shi kuma  suka  ji masa  ciwo  a kafa,  wanda ya  nuna  muna, inda ya ce  tun daga  lokacin ne  ya ga  akwai  bukatar  ya mallaki  bindigogi  domin gudun  bacin rana.
Ya kuma tabbatar da cewa an sayar masa bindigogin a kan Naira dubu 350.

…Gwamnan Oyo ya yaba wa ’yan sanda kan kamun

Kabir Yayo Ali, Daga Ibadan

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya jinjina wa ’yan sanda da suka kama tsohon shugaban bangaren kungiyar direbobi (NURTW) na jihar, Alhaji Mukaila Lamidi da ake yi wa lakabi da ‘Audiliary’, wanda ake zargin bangarensa da bangaren Lateef Oloruntoki, mai lakabin Tokyo da hannu wajen kashe Malam Bala Usman Shanono, shugaban kungiyar dalibai, sashen kiwon lafiya na Jami’ar Ahmadu Bello, cikin watan Yunin shekarar 2011 a Ibadan.
A wancan lokaci ne Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Oyo ta yi alkawarin bayar da kyautar Naira dubu dari biyar ga dukkan wanda ya ba ta labarin maboyar wadannan shugabanni biyu da ake nemansu ruwa a jallo, domin tuhumarsu da laifin kisan gilla a dalilin barkewar tarzoma a tsakanin magoya bayansu da ta yi sanadin mutuwar Bala Usman Shanono da wasu mutane masu yawan.
Jinjinar dai tana cikin wata takardar sanarwa da mai ba shi shawara na musamman a kan kafofin labarai, Dokta Festus Adedayo ya sanya wa hannu, inda Gwamna Abiola ya ce, “’Yan sandan da suka kamo wannan mutum sun cancanci yabo kuma akwai alamar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar”.