Tsohon Shugaban Majalisar Kano ya nemi kotu ta kwato masa filinsa
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Abdullahi Abubakar karaye ya yi karar fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Aminu dantata da wani dan sanda mai suna Bilal Muhamamd da Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya Alhaji Tambari Yabo Muhamad a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, […]
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Abdullahi Abubakar karaye ya yi karar fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Aminu dantata da wani dan sanda mai suna Bilal Muhamamd da Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya Alhaji Tambari Yabo Muhamad a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, bisa zarginsu da kokarin kwace masa filinsa kwaya daya da ke kan titin UDB, a Unguwar Nasarawa GRA a birnin Kano.
Takardar karar da tsohon shugaban majalisar ta bayyana cewa tana neman kotu ta yi masa tsakani da ’yan sandan ofishin Mataimakin Sufeton game da barazana da yunkurin kamu da suke yi ga iyalin tsohon shugaban majalisar. Har ila yau takardar ta nemi kotun da ta dakatar da wanda ake kara na farko da na biyu da bayyana kansu a matsayin wadanda suka mallaki wannan filin.
Alkalin kotun, Mai shari’a Lawal Wada Mahmud ya bayar da umarnin dakatar da daga duk wata magana ko ci gaba da yin gini a filin, har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci a kan karar. Sannan ya dage sauraren karar zuwa ranar 6 ga watan gobe.